Najeriya: SERAP Ta Bukaci Kotu Ta Bawa Shugaba Buhari Umarnin Wallafa Bashin Da Akebin Kasar

20200803_193929
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar SERAP ta bukaci babbar kotun tarrayya data bawa shugaba buhari umarnin wallafa basussukan da ake bin gwamnatin kasar tun daga shekarar 2015.‎

Kungiyar ta bukaci kotun data sa shugaba Buhari ya bayyana yawan kudin da gwamnatin ta karbo, akan nawa?, da kuma ayyukan da aka gudanar aka kashe kudaden.

Kuma sun bukaci Abubakar Malami babban akanta na kasa, ministar kudi da tsare tsare Zainab Ahmed da Patience Oniha Darakta janaral ta ma’akatar basuka na cikin wadan da kungiya ta maka a kotu.

Haka nan ‎SERAP ta bukaci kotu data sa shugaba Buhari ya fadawa yan Najeriya sunayen kasashen da suka bada basussuka, da yarjejeniyar da akayi da kuma idan akwai wadanda suka karbi cin hanci yayin yarjejeniyar bashin.

San nan sun bukaci kotu data sa shugaban kasar ya bayyanawa yan Najeriya idan zaisa hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC su duba yadda aka kasha kudaden da aka ranto dun daga 29 ga watan Mayu na shekarar 2015.

Haka nan SERAP tace idan babu gaskiya wajen kashe kudaden hakan zai sa ‘yan Najeriya su yanke kauna daga ayyukan da akeyi.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply