Najeriya: Rundunar Yansandan Jihar Kano Tace Ta Kama Dilolin Kwayoyi Da Kuma Yan Daba 1,583 Cikin Watanni 8

police-logo1
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar yansandan jihar Kano tace ta kama mutane 1,583 da ake zargi da sai da kwayoyi da kuma wasu laifuka a wata 8 da suka gabata a jihar.

Kwamishinan yansandan jihar Mr Habu Ahmad ne ya bayyana hakan a rahoton daya fitar tab akin mai Magana da yawun rundunar DSP Abdullahi Haruna a Kano.

Kwamishinan ya bayyana hakan yayin da babban Daraktan League for Societal Protection Against Drug Abuse ya kai masa ziyara a ofishinsa dake kano.

Ahmad ya bayyana cewa 1,545 yan daba ne sai kuma dilolin kwayoyi 38 a hlokuta daban-daban daga watan Nuwamba na shekarar 2019 zuwa watan Yuli na 2020.

Haka nan yace rundunar ta kwato makamai 1, 555 Machetes, kullin tabar wiwi 1, 689, katan din codeine 11 da kuma katan 518 na wasu kayan maye.

Kwamishinan yace sun samu nasarar cafke su bayan rahotanni da suka samu daga sashin su dake kakkabe ayyukan masu laifuka a jihar.

San nan Ahmad ya jaddada kokarinsu na hadin gwiwa tsakaninsu da kungiyoyi da yankuna don karfafa kawo karshen laifuka da hadin kan jama’a a jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply