Najeriya: Rundunar Yansandan Jihar Gombe Sun Kama Masu Kwacen Babura Guda 6

Nigerian-police-thumb
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar yansandan jiahr Gombe sun bayyana cewa sun kama mutane 6 da ake zargi da gudanar da ayyukan ta’addanci, kwacen babaura a Gombe.

Wadanda ake zargin sune Adamu Aliyu, 62, Abdulrahaman Ibrahim, 26 yan kauyen Kwadon a karamar hukumar Yemaltu-Deba da Usman Mohammed Gidado, 24yrs, Mohammed Sale, 22 and Mohammed Abbas, 18 duk daga unguwar Bomala a cikin garin Gombe.

An kama wadanda ake zargin ranar Lahadi da daddare yayin da jami’an State Intelligent Bureausuke sunturi. Rahoton da rundunar ta fitarwa manema labarai yace jami’ar hulda da jama’ata rundunar SP. Obed Mary Malum c eta fitar da sanarwar inda tace an kama su bayan samun bayanan sirri da kuma samun mashina masu kafa uku inda suka tabbatar na sata ne inda suke kwata ko suke amfani da masta key.

Haka nan tace an kama wani mai suna Mohammed Haruna, 49 daga garin Bidda dake jihar Niger da kuma wani Femi Benjamin dan shekaru 30 a kan titin unity road dake Kabba a jihar Kogi bayan day a hada kai da karbar kaya ba bisa ka’ida ba a jihar Gombe.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply