Najeriya: Rundunar Yansandan Jihar Adamawa Sun Kama Wanda Yayiwa Yar Shekaru 9 Fyade

the-nigerian-police-360x240
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar yansandan jihar Adamawa sun kama wani mai suna Obiora Patrick dan shekaru 39 mazauni titin Hospital road dake Jimeta a karamar hukumar Yola ta Arewa bayan da yayiwa wata yarinya yar shekaru 9 fyade.

DSP Suleiman Yahaya Nguroje mai Magana da yawun rundunar da hulda da jama’a ne ya bayyana hakan inda yace ana kan binciken lafiyar yarinyar.

Rahoton yace rundunar tayi kira ga jama’a dasu tashi wajen yaki da fyaden ga mata da yara san nan sun yi kira ga iyaye dasu dinga kula da yaran dake gabansu.

San nnan su bayyana kokarinsu na da jajircewarsu wajen kare lafiyar mutane da dukiyoyinsu, san nan sunyi kira da dinga bayyana musu duk wanda aka gani ba a yadda dashi ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply