Najeriya: Ministan Ilimi Yace Ma’aikatar Ilimi Baza Ta Dauki Kasadar Bude Makarantu Ba

schools
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan ilimi yace ma’aikatar ilimi baza ta dauki kasadar bude makarantu ba har sai an shawo kan annobar COVID-19.
Mr Emeka Nwajiuba ya bayyana hakan yayin taron da ake na kullum na kwamitin yaki da cutar na kasa .

Ministan ya bayyana cewa baza su bude makarantun ba har sai gwamnati ta tabbatar da cewa yara na cikin kariya bazasu kamu cutar ta coronavirus ba ko wasu su shafawa wasu.

Ya kara da cewa zasu hada kai da kungiyar lafiya ta duniya kafin a bude makarantun, inda zasu wallafa matakan abubuwan da ya kamata makarantun su dauka na gwamnati dana kudi.

Nwajiuba ya bayyana cewa manyan makarantu zasu dinga yin zango cikin zango inda wasu zasu rarraba su wasu a zangon farko wasu a mai binshi saboda a rage cunkoso.

Haka nan yayi kira ga malaman manyan makarantu dasu yi amfani da wannan lokacin su habbaka kansu da abubuwan day a kamata.

San nan yace daliban makarantun Sakandire manyan zasu riga komawa kafin yan kasa dasu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply