Najeriya: Mazauna Garin Jalingo Sunyi Kira Ga Shugaba Buhari Da Yayi Bincike Kan Aikin Titin Numan Zuwa Jalingo

taraba-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Majauna garin Jalingo dake jihar Taraba a gabashin najeriya sunyi tururwa a titunan jihar inda suke kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari da yasa baki kan aikin gyaran hanyar Numan zuwa Jalingo.

Mai rahoton mu na yankin ya bayyana mana cewa sun gudanar da zanga-zangar lumana wanda aka farad a karfe 10 na safiyar Asabar wanda Mr. Ishaq Alkasim ya jagoranta zuwa ma’aikatar ayyuka ta jihar dake Jalingo.

Mrs. Ishaq Alkassim yayin da yake yiwa manema labarai jawabi yace suna kira ga shugaban kasa day a bincika aikin baki daya.

Haka nan yace idan za’a iya tunawa an bawa kamfanin DEUX project Nig. Ltd aikin ranar 24 g awatan Yuli na shekarar kan Naira biliyan 11 wanda suka ce zasu kammala kan watanni 20 wanda har yanzu babau cigaba.

San nan yace hanyar mai nisan kilomita 104 ta samar da matsalar tattalin arziki da cigaban jihar.

Haka nan yace saboda rashin kyan hanyar matafiya najin tsoro saboda masu garkuwa da mutane, yan fashi da masu aikata mugggan laifuka na yawan amfani da hanyar.

San nan yayi kira ga ministan ayyuka da gidaje Mr. Babatunde Fashola daya kawo musu dauki.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply