Najeriya: Mazauna Birnin Maiduguri Sun Koka Kan Farashin Raguna

ram
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Juliet Bada and Charity Amos, Maiduguri

‘Yan kasuwar dabbobi dake birnin Maiduguri sun bayyana rashin jin dadinsu kan yadda farashin raguna ya tashi saboda gabatowar babbar sallah a kasuwanni.

Alhaji Abdullahi Wazirin kasuwar dabbobin ya danganta hakan da bullar cutar coronovirus a jihar wanda yayi sanadiyyar kulle iyakokin kasar har ba’a iya shigo da dabbobin daga kasashen da ake makotaka dasu kamar Chadi, Nijar da kuma Kamaru.

Haka nan yace ayyukan yan kungiyar Boko Haram a yankin na Arewa Maso gabas yasa manoma basa iya kiwon dabbobi saboda tsoron a kasha su yayin kiwon ko ayi awon gaba da dabbobin.

Wani mai suna Bukar Wakil ya roki gwamnatin gwamnati ta ko wane mataki data taimaka da shingen jami’an tsaro a kan titunan Monguno, Banki da Ganboru Ngala ta kuma kara sumu ranakun da jami’an tsaro suke raka matafiya don rage karancin dabbobin.

Wakil ya kara da cewa ya jinjinawa gwamnan jihar farfesa Babgana Umara Zulum da shugaban sojin kasa Lt. Gen. Tukur Buratai kan yadda suka jairce wajen yaki da ta’addanci.

San nan ya roki gwamnati data taimaka musu da kasar ciko da kuma magudanan ruwa a mayankar abbatuwa.
Dandal Kura Radio ta rawaito cewa an samu karuwar farashin sakamakon gabatowar sallar saboda yadda ake sayan ragunan a jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply