
Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo zai karbi shugabancin rikon kwarya daga gobe ranar jumma’a a yayin da shugaban kasar ta Najeriya Muhammadu Buhari zai fara hutunsa na kwanaki 10 a kasar waje.
Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar Femi Adesina shi ya bayyana hakan yayin mika wasikar tafiyan shugaba Buhari ga majalisun kasar abisa dokar da kundun tsarin kasa na alip dari tara da chasa’in da tara karkashin sashe na 145 taba da damar yin haka.
A watan Mayu na shekarar 2018 shugaba Buharin ya ziyarci kasar London domin binciken lafiyarsa.
