Najeriya: Masu Wa’azi, Masu haihuwa, Wandanda Zasuyi Aure Zasu Fara Biyan Haraji A Jihar Gombe

gombe small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An bayyana cewa Hukumar haraji ta jihar Gombe zata fadada biyan haraji a jihar inda wadanda zasuyi rigista sun hada da kungiyoyin addinai, masu zama a jihar, masu kiwo da sauransu.

Yunkurin yasha cece-kuce da suka dama daga jama’a bayan da aka buga a shafin sada zumunta na Facebook inda akace kimanin 50 ne suka karu da zasu fara biyan haraji a jihar da hadin gwiwar kananan hukumomin jihar.

Rahoton yace masu yin wa’azi a fili zasu biya N5,000 na yin rigista, N10,000 na rigistar aure, N5,000 na rigistar haihuwa.

Ragowar sune N1,000 Radio da Talabijin, N1,000 na keke, N1,000 na masu baro, kwale-kwale 500, 1,500 dabbobi, 1,000 na masu tebura, 12,000 masu yanka shanu da rakuma, shagunan abinci da gidan biredi N25,000, allunan kan titi N150,000 sai kuma kudin tsaftace muhalli N3,000.

Mutane da dama sun koka da wan nan harajin idan aka duba yadda aka samu matsalar tattalin arziki a kasar inda mutane ke cikin matsi sakamon annobar Coronavirus wadda ta shafi mutane da dama.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply