
Hukumar kula da magunguna da kayan abinci wato NAFDAC tace hakkinta ne ta taimakawa duk wani wanda yake da niyyar samar da maganin COVID-19.
Darakta Ganaral ta hukumar farfesa Mojisola Adeyeye ne ya bayyana hakan a rahoton day a fitar a Abuja. Adeyeye tace a kokarin su an kafa kwamitin magungunan gargajiya don sarrafa magungunan ta cutar COVID-19.
Tace kwamitin zai hada da masu sarrafawa, malaman jami’a, masu bincike, da kuma masu ruwa da tsaki wajen cike guraben da ake dasu tsakanin masu ilimin maganin gargajiya da masu sarrafa shi.

Tace hakan hakan zai bada hadin kai, da bunkasa kasuwanci da kuma samun sahihan magunguna masu inganci.
Haka nan kwamitin ya gana da mambobinsa sau 3 tunda aka kafa shi ranar 15 ga watan Maris da 6 ga watan Satumba na shekarar 2019 sai kuma a kwanakin nan ranar 8 ga watan Mayu na wan nan 2020.
