
Kwararrun masana tsaro a Najeriya karkashin kungiyar Amurka ta tsaro sun bayyana cewa yadda gwamnatin Najeriya ke tafiyar da sha’anin Boko Haram da rikicin manoma da makiyaya ne zai nuna ko za’ayi zaben 2019 ko baza ayi ba kamar yadda aka shirya.
Shugabar AAC Dame Victoria Ekhomu ta bayyana kafin taron da za’ayi na tsaro a jihar Legas cewa ya kamata gwamnati tayi tunani kan lamarin don ta gano yadda za’a shawo kan sha’anin tsaron.
Ekhomu ta kara da cewa rikice-rikicen da ke faruwa yayi sanadiyyar mutuwar mutane da dama Wasu kuma da yawa baza su iya cigaba da sana’oin da suka saba yi ba, don haka idan ba’a dauki mataki ba zai shafi zaben da za’a gudanar.
Haka nan ta kirayi gwamnati data yi amfani da dabarun kimiyya don gano dalilin da yasa wadan nan yan ta’addan suke ayyukansu da inda suke samun kudade don daukar mataki kafin zabe.
