Najeriya: Manjo Janar AM Dikko Ya zama Sabon Kwamandan Operation Lafiya Dole

AM Dikko
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rundunar sojin Najeriya ta yi wa wasu kwamandojinta sauye-sauyen wurin aiki domin cigaba da ya’kar ta’addancin maya’kan Boko Haram, sanarwar hakan ya kuma ce wadanda aka yi wa sauyin mu‘kamin sun hada da manyan kwamandoji da kuma sauran mu‘kamai daban-daban na hukumar sojin.

Sauye-sauyen ya shafi dukkanin bangarorin jami’an sojin wadanda suke jan ragamar yaki ta ta’addanci. Hakazalika sauyin ya shafi kwamandan soji mai kula shiyyar Operation Lafiya Dole, babban manufar yin sauye-sauyen dai shi ne bai wa sabbin jami’an sojin damar nasu dabarun yaki da ta’addanci kamar yadda shugaban hafsan sojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ya bayyana don tabbatar da tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sanarwar ta fito daga jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin Janar Taxas Chukwu, inda ya ce wadanda sauye-sauyen ya shafa sun hada da Manjo Janar AM Dikko, wadda yamaye gurbin kwamandan Operation Lafiya Dole. Har ila yau sauyin ya shafi Manjo Janar Lucky Irabo na rundunar sojin kasa da kasa da ke samar da zaman lafiya kan iyakokin kasashe biyar da ke yankin tabkin Chadi, dukkanin sauye-sauyen dai za su fara aiki daga ranar 1 ga watan Agustan wannan shekarar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply