Najeriya: Ma’aikatan Kiwon Lafiya 16 Sun Kamu Da Cutar Corona A JIhar Borno

covid
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno tace kimanin ma’aikatan lafiya 16 ne suka kamu da cutar COVID-19 tunda aka samu barkewar cutar a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar kuma sakataren kwamitin yaki da cutar Dr. Salihu Kwaya-Bura ne ya bayyana hakan a Maiduguri yayin yiwa manema labarai bayani kan annobar wanda kwamitin karta kwana na yaki da cutar yakeyi.

Kwaya-Bura yace hakan ya nuna yadda ake samun Karin ma’aikatan kiwon lafiya na kamuwa da cutar yayin yaki da cutar.

Haka nan ya kara da cewa an dauki kwararan matakai wajen kare ma’aikatan lafiya inda yace jihar tayi odar kayan kariya 2000. Inda yace mutane 69 ne suka kamu da cutar a jihar sai mutum 9 da suka rasa rayukansu.
Kwaya-Bura yace a yanzu haka bau wani mara lafiya da yake cikin yanayi mai tsanani, suna nan a wajen killace marasa lafiya suna samun kulawa duk da kowanne ya danganta da irin kulawar da yake samu don wani yafi na wani.

Haka nan Kwaya-Bura yace sun kara masu gudanar da ayyukan inda masu binciko masu cutar 25 da kuma masu karbar rahotanni guda 5.
Shugaban kwamitin kuma mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Kadafur yace kwamitin bai samu damar bada bayanai ranar alhamis da juma’a ba sakamakon abbuwan da suka sha kansu na kokarin fadadainda ake killace mutane inda suke sa ran daga gadaje 100 zasu maida su 500 zuwa 1000.

Haka na yayi kira ga jama’a dasu dinga bin dokokin kariya kan cutar musamman wajen zaman gida, bada tazara, sa takunkumin fuska da kuma yawan wanke hannu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply