Najeriya: Leah Sharibu Ta Roki Shugaban Najeriya Daya Ceto ta Daga Hannun Boko Haram

leah sharibu
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Cikin wani sakon murya da dalibar makarantar Dapchi mai suna Leah Sharibu, ta fitar ta nemi agajin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya ku6utar da ita daga hannun maya’kan Boko Haram.

Sharibu, ta yi magana na tsawun dakika 35 cikin harshen Hausa, inda ta yi ‘kira ga gwamnatin Najeriya da kuma wadanda suka damu da ita domin ceto ta daga halin da take ciki.

Idan za a iya tunawa dai Leah Sharibu ita ce daliba daya tilo Kirista daga cikin d’alibai 119 da maya’kan Boko Haram suka yi garkuwa da su daga makarantar gwamnati ta kwana na garin Dapchi, dake jihar Yobe a ranar 19 ga watan Faburairun da ya gabata.

Ya zuwa yanzu dai fadar shugaban ‘kasar Najeriya ba ta ce komai game da muryar d’alibar ba, amma shugaba Muhammadu Buhari ya bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ceto dukkannin wadanda maya’kan Boko Haram suka yi garkuwa da su, amma a halin yanzu jami’an tsaron farin kaya na DSS za su yi bincike kan muryar da ake fidda da sunan Leah.

Shima a nasa ban6aren kakakin shugaban ‘kasaR kan harkokin yad’a labarai Malam Garba Shehu, ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa gwamnati na sane da irin halin da Leah ke ciki, don haka gwamnati za ta iyaka iyawarta domin ganin an ceto dukkanin wadanda maya’kan suka yi garkuwa da su.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply