Najeriya: Kungiyar Yan Jaridu Tayi Allah Wadai Da Cin Zarafin Dan Kungiyar A Taraba

NUJ
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar yan jaridu reshen jihar Taraba sunyi alla wadai da yadda wata kotu dake zamanta a Jalingo taci zarafin wani dan kungiyarsu.

Shugaban reshen jihar Comrade Jovita Shafe ne ya bayyana hakan a taron da suka gudanar a cibiyar su dake jihar yayin kaddammar da sababbin ma’aikatan kungiyarna jihar.

Shafe ya bayyana wan nan a matsayin abin takaicin da babbar kotun ta jalingo tayi yayin da dagacin kauyen Karim Lawan na karamar hukumar Karim Lamido Alh. Mohammed Topi wanda yakai karar mabiyansa su 19 in aka hana dan jaridar daukar labaran aka koreshi daga kotun.

Shugaban yace idan aka kara yi musu irin wan nan kungiyarsu baza ta yadda ba inda yace yan jarida hanya ne na cigaban alumma bawai abin da zaka hau bane in kana da bukata.

Ahaka nan yace sabanin da aka samu tsakanin lauyan dad an jaridar a kotun bai cancanta ba kuma dole su gudanar da aiki ba tare da yi musu iyaka ba.

San nan binciken da suka gudanar ya nuna cewa dagacin kauyen nan Karim Lawan Alh. Mohammed Topi baya adalci kuma yana kwace gonakin mutane dana kifaye ba bisa ka’ida ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply