Najeriya: Kungiyar Mata Lauyoyi Tayi Kira Da A Dinga Yankewa Masu Fyade Hukuncin Kisa

FIIDA
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar mata lauyoyi ta duniya wato International Federation of Women Lawyers reshen jihar Plateau Babban bankin Najeriya ya bayyana cewa kasar ta samu Karin Dala Biliyan sun yi kira da a dinga gudanar da kukuncin kisa ga masu fyade a kasar nan.

Shugabar kungiyar ta jihar Plateau Mrs Mary Izam c eta bayyana hakan ga manema labarai a Jos, inda tace idan aka kafa hukuncin kisa ga masu fyade za’a samu a dakile mummunan aikin a kasar.

San nan tace fyade kamar kisa ne tun da masu fyaden yawanci suna kasha wadanda suka yiwa ko kuma su kasha musu tunaninsu da hankalinsu.

Haka nan ta bayyana cewa a dokar miyagun laifuka fyade na cikin manyan laifuka, kuma ya kamata a daukeshi da kwakkwaran hukunci wanda zai ja hanakalin masu aikata shi.

Ta kara da cewa ya kamata hukuncin fyade ya zama bai daya bawai ko wane alkali ya yanke hukunshi daban a kotun da yake ba.
Izam ta bayyana takaicin tan a yadda ake boye laifukan fyade saboda iyaye, masu kula da yara suke boye abubuwan dake faruwa don kare yaransu dasu kansu daga kyamatar da jama’a zasuyi musu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply