Najeriya: Kungiyar Kwadago Sun Bawa Gwamnatin Jihar Kano Wa’adin Kwana 14

nlc2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar kwadago ta bawa gwamnatin jihar Kano wa’adin kwana 14 kan yanke albashin ma’aikata datayi daga watan Mayu.
Dandal Kura Radio ta gano cewa gwamnatin jihar Kano ta yanke albashin ma’aikata na watan Mayu inda ta danganta shi da sakamakon annobar COVID-19.

Duk da dai babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar na yanke albashin, majiyar mu ta bayyana mana cewa gwamanatin jihar Kano ta maida tsohon albashi na N18, 000 maimakon N30,000.

Haka nan Dandal Kura Radio ya gano cewa yawancin ma’aikata sun snuna mamakinsu yayin da suka samu albashin watan Mayu bayan da suka lura an cire musu kimanin kashi 20.

Yayin da yake ganawa da manema labarai shugaban yan kwadago na jihar Comrade Kabiru Ado Minjibir yace gwamanyatin ta karya dokar bada kayyadajjen albashi ta 2019 wanda kwamitin yan majalisu ya tabbatar kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa hannu.

Haka nan ya bayyana mamakinsa na yanke albashin ma’aikatan ba tare da sanin kungiyar tasu ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply