Najeriya: Kotu Ta Ba Yan Majalisa Damar Cigaba da Yunkurin Tsige Shugaba Buhari

buhari-talkingsmall
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wata babbar kotu dake zamanta a garin Osogbo dake jihar Osun a yammacin najeriya ta bawa majalisun kasar damar cigaba da yunkurin tsige shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Justice Maurine Adaobi Onyetenu ne ya bada damar bayan da wasu yan kasar 2 suka shigar da karar, mutanen 2 sune Kanmi Ajibola lauya kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam da Sulaiman Adeniyi inda suka bukaci kotun data bawa yan majalisun damar tsige shugaba Buharin.

Masu karar sun rubutawa majalisun wata 3 da suka wuce kan bukatar a tsige shugaban kasar, inda suka bada misalai na karya dokar kasa da shugaban yayi. Amma bayan da yan majalisun basu dauki mataki ba shine Ajibola and Adeniyi suka kai kara babbar kotu ta Osogbo kan suna neman kotu ta bawa majalisun dama kan tsige shugaban.

Sun bayyana cewa shugaban ya karya dokar kasa a kundin tsarin mulki na shekarar 1999, inda ya tsaya zabe, yaci kuma aka rantsar dashi ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2015 ba tare da mallakar takardun da suka dace ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply