Najeriya: Komanda Ya Bukaci Da A Duba Yadda Kungiyoyi Ke Bawa Yan Gudun Hijira Taimako

army
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo Janaral Abba Dikko ya jaddada bukatar a duba yadda kungiyoyi masu zaman kansu suke bawa yan gudun hijira taimako a arewa maso gabashin Najeriya.

Shugaban ya bayyana hakan yayin da mataimakiyar shugaban kwamishinan burtaniya Harriett Thomson takai ziyara hedikwatar su dake Maimalari a Maiduguri. Janaral Dikko ya kara da cewa duk da akwai kungiyoyi da dama na gida dana kasashen waje dasuke bada taimako a Arewa maso gabashin Najeriya, ya kamata a dinga duba al’adun mutanen yankin.

Haka zalika ya tabbatar da cewa rundunar Operation Lafiya Dole zata cigaba da bawa kungiyoyin hadin kai don ci gaban yankin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply