Najeriya: Kimanin Yansandan Kwantar Da Tarzoma 400 Suka Gudanar Da Zanga-Zanga A Maiduguri

police
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kimanin yansandan kwantar da tarzoma 400 suka gudanar da zanga-zangar lumana a hedikwatarsu dake jihar Borno a Arewa maso gabashin Najeriya ranar litinin, kan a kyautata musu ta fannin ayyukansu da wasu hakkokinsu da ba’a biyasu ba.

Yansandan masu zanga zangar sunyi ta harbe-harbe a iska inda daga bisani suka rufe titin jos dake cikin birnin Maiduguri da hana mutane wucewa na kimaninin awannni biyar.

Zanga zangar tayi sanadiyar hana dalibai zuwa makarantunsu ciki harda babban makaranta ta Ramat da kwalejin sir kashim. Hakan yasa mutane da dama komawa gidajensu.

Masu zanga zangar na ikirarin cewa ana biyan sojoji da yan kungiyar sa kai na CJTF hakkokinsu amma su an watsar dasu.

Mazauna birni na Maiduguri sun bayyana damuwarsu inda suka ce idan ba’a dauki matakin gaggawa ba hakan zai sa yan ta’addan da suke kusa su samu dama.

Anyi kokarin jin ta bakin mai hulda da jama’a na rundunar yansandan ta wayar tarho amma ba’a dauki wayar ba haka zalika ta shafinsu na yanar gizo inda aka aika musu sako amma basu bada amsa ba.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply