Najeriya: Kimanin Rumfunan Yan Gudun Hijira 3000 Ne Suka Rushe Sakamakon Iska Mai Karfi A Maiduguri

idps
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ruwan sama da iska mai karfi sun wanda yayi sanadiyar ambaliya sun a sansanonin yan gudun hijira guda usk dake birnin lalata kimanin rumfunan yan gudun hijira 3,000 dake birnin Maiduguri.

Haka nan Sunyi sanadiyar rasa matsungunan wasu magidantan a sansanin dake filin wasa na Muhammadu Buhari da Kawar Maila duk a Maiduguri.

Manajan sansanin yan gudun hijira na filin wasa na Mohammed Goni Hauwa Njogole ta bayyanawa shugabar hukumar bata agaji ta kasa wato Hajiya Yabawa Kolo yayin data kai musu ziyara cewa sama da rumfuna 2,293 ne suka lalace sakamakon ruwan.

Haka nan Njogole tace an kafa sansanin 27 ga watan fabarairu na shekarar 2019 sakamaon hare-haren da yasa mutane suka baro Baga da kuma karamar hukumar Kukawa.

Ta kara da cewa sansanin nada magidanta 3,574 inda ake fa mutane kimanin su 15,957.

Sai kuma 887 da suka zo daga Konduga, Auno, Kayamla da kauyukan ddake kewayensu.

Hajiya Yabawa Kolo ta danganta ambaliyar da yanayin gurin inda tace kwanan nan zai wuce don gwamnati na nan na shirye shirye na musamman.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply