Najeriya: KAROTA Ta Kama Magunguna Marasa Lambar NAFDAC A Kano

KAROTA
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kungiyar kula da tituna da cinkoso ta jihar Kano wato ano KAROTA ta kama magungunan jabu na kimanin miliyan 25 a unguwar has Sabon Gari dake karamar hukumar Fagge.

Sun kama Maganin mai suna Arofranil wanda ake sha don karfin saduwa ga maza bayan rahoton da suka samu na sirri cewa maganin bashida lambar NAFDAC.

Rahoton ya fito daga bakin mai hulda da jama’a na kungiyar Nabilusi Abubakar K/Na’isa wanda wakilinmu daga Kano ya hada mana inda yace an kama magungunan a Sabon Gari a tashar dake kan titin New Road yayin da motar da take makare da magungunan take shirin rabawa.

Rahoton yace an samu kwalaye kimanin 5000 na maganin wanda tuni kunggiyar sukayi awon gaba dasu amma basu samu nasarar kama mai kayan ba sakamakon tserewa da yayi.

Kamar yadda kungiyar KAROTA ta saba zata mika magungunan ga kwamitin yaki da magungunan jabu karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar don daukar mataki.

Manajan Daraktan kungiyar Baffa Babba Dan’agundi yayi kira ga jamaa dasu dinga taimakawa kungiyar don ta dinga samu ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply