Najeriya: Jihar Kaduna Ta Maida Almajirai 35,000 Jihohinsu

Kaduna
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnantin jihar Kaduna ta mayar da almajirai 35,000 zuwa jihohi 17 da kuma kasashen dake makotaka da Najeriya.

Hajiya Hafsat Baba kwamishinar kula da mutane da walwalar jama’a c eta bayyana hakan a hirar tag a manema labarai inda tace suma sun karbi kimanin almajirai 1,000 daga wasu jihohin.

Baba ta bayyanna cewa gwamnati ta dauki matakin tabbatar da cewa yaran sun samu ilimin Qurani dana boko karkashin kulawar iyayensu.
Haka nan tace da taimakon kungiyar UNICEF, ma’aikatar ta zata wayar da kan yaran da kuma duba lafiyar Almajiran da aka dawo dasu daga wasu jihohin.

Tace banda ma annobar COVID-19, wasu daga cikin Almajiran nada kuraje da wasu cututtuka da za’a basa magunguna kafin a mika su iyayensu.
San nan tace ma’aikatar ta zata cigaba das a sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki a yankuna ta yadda za’a nuna musu cewa iyaye ya kamata su kula da yayansu.

Gwamnan jihar malam Nasir El-Rufa’i a kwanankin nan yayi wa iyaye gargadi cewa duk wanda ya kara kai danshi Almajiranci za’a kaishi gidan yari ya zauna na shekaru biyu

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply