Najeriya: Jihar Adamawa Nada LIkitoci 300 Kacal

ADAMAWA
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kungiyar likitocin Nigeria reshen jihar Adamawa Dr Tonde Gargah yace duk da yawan mutanen Adamawa su miliyan hudu sunada likitoci 300 ne kacal da zasu kula da lafiyarsu.

Dr Gargah, ya bayyana hakan ranar Damokaradiyya a jihar yayin da aka gudanar da taro a Yola. Yace yawan likitocin jihar yayi kadan kan yadda hukumar lafiya ta duniya ta bukaci cewa ko wane likita zai kula da kimanin mutane 600.

Amma a yanzu idan aka kiyasta da yawan mutanen jihar ko wane likita daya na kula da kimanin mutane 13,300 wanda hakan yayi kadan, kuma idan aka kwatatnta masu kiwon lafiyar da makotansu na yanki za’a ga basa samun yadda takwarorinsu suke samu.

Haka nan yayi kira ga gwamnatin jihar data duba jin dadi da walwalar likitocin don ta karfafa musu gwiwa su gudanar da ayyukan day a kamata.

Gargah ya lura cewa adadain yan jihar Adamawa na karuwa a kowane lokaci musamman a kudancin kananan hukumomin yankin Yola, kuma yayi kira g gwamnati data kara gina asibitoci don habbaka kiwon lafiya a jihar.
Yayin da yake maida martini Gwamnan jihar Ahmadu Fintiri yace cikin shekara daya gwamantinsa ta gudanar da ayyukan more rayuwa da zasu habbaka rayuwar mutanen jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply