
Rundunar Sojin saman na Najeriya karkashin shirin Operation HADARIN DAJI sun lalata matsugunan yan bindiga da kuma kashashe kimanin 30 a harin da suka kai musu ta sama a jiya a dajin Doumborou dake jihar Zamfara.
Rahoton ya fito daga mai kula da harkar yada labarai na rundunar Major General John Enenche inda yace an gudanar da aikin ta hanyar samun bayanan sirri daga mutane inda suka samu rahoton cewa suna amfani da dajin wajen aje kayansu.
Haka nan jirginsu na leken asiri ya gano musu inda yan bindigar suke da mashinan su da kuma inda suke ajiye kayayyakin, inda daga nan suka samu nasarar lalata dakunanan ajiyar.

Shugaban rundunar sojin saman ya yabawa Operation HADARIN DAJI kan nuna kwarewar da sukayi wajen gudanar da wannan aikin inda yace suna kokari da sojojin kasa wajen kakkabe yan bindigar gaba daya.
