Najeriya: INEC Tace Tana Jiran Amsa Daga Majalisun Kasar Kan Wasu Gurabe

inec
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC tace tana jiran amsa daga majalisar kasar kan wasu gurabe a majalisar.

Shugaban hukumar Professor Mahmood Yakubu ya fadi hakan ne a wani taro da ya shirya tare da yan jaridu a Jahar legas na kasar inda yace akwai kimanain zabubbuka 5 da za’a cike guraben amma bazai iya ba har sai an tabbatar da babau masu guraben.

Ya kara da cewa dokar INEC na amfani ne na da idan mai kula da zaben yace kai ne kaci zaben kotu ce kadai zata iya kwacewa.

Haka nan Professor Yakubu aya bayyana cewa hukumar ta kara canza fasalin katin zaben don a a samu madadin na’urar gudanar da zaben musamman mutanen da hannunsu baya dauka.

Ya kuma kara da cewa duk da matsalar tsaro hukumar ta samu mutane da dama a jihohin Borno da Benue, inda yace yafi sauki ma ayiwa rigistar a matsugunan ya gudun hijira kan a guraren dake yankunansu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply