
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Najeriya wato INEC ta sanar cewa an kammala zaben gwamna a jihar Ekiti ranar Asabar data gabata cikin lumana.
Daraktan yada labarai da ilimantar da al umma kan sha’anin zabe na INEC Oluwole Osaze –Uzzi shine ya sanar da hakan ta wayar tarho lokacin da yake ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nigeria wato NAN.
Daraktan ya nuna jin dadin sa ainun kan yadda aka fara zaben a kan lokaci a akasarin mazabu, ya kuma kara da cewa hukumar zata yi aiki kai da fata domin magance masalar na’urorin tantancewa kafin zaben gama gari na 2019 a cikin kasar.
Uzzi har ila yau, ya jinjinwa masu ruwa da tsaki kan irin rawar da suka taka ayayin wannan zaben.
