Najeriya: Hukumar NDLEA Sun Kama Soja Da Makamai A Jihar Yobe

ndlea large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An kama wani soja dan shekaru 25 mai suna Mohammed Kashim a jihar Yobe da makamai da kuma tabar wiwi.

Ma’aikatan hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA ne suka kama shi a titin Nguru/Hadeja .

Mataimakin kwamandan hukumar na jihar Yobe Mr. Julius Zer ne ya bayyana hakan inda yace an kamashi da makamai 30, da bindigar magazine da kuma tabar wiwi mai nayin kilo 1.

Haka nan yace sun gano cewa sojan dan asalin karamar hukumar Geidam ne ta jihar Yobe wanda yake aiki da rundunar sojin Najeriya dake Oyo a jihar Ibadan inda ya taho don bikin Sallah.

Haka nan sun kama shi cikin babbar mota a hanyar shit a zuwa garin na Geidam.

Tuni da dai suka mika sojan da makaman ga shugaban yansandan dake Nguru.

Mai Magana da yawun rundunar yansandan yankin T ASP Dungus Abdulkareem yace basu samu labara ba amma zasu bayyanawa manema labarai da zarar sun samu cikakkaen bayani bayan bikin Sallah.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply