Najeriya: Gwamnatin Tarayya Zata Fara Biyan Masu Sana’ar Hannu N30,000

images (8)
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya tace zata fara biyan yan Najeriya naira 30,000 masu aikin hannu kimanin su 330,000 a fadin kasar karkashin tsarin habbaka tattalin arziki.

Babban mataimakin mataimakin shugaban kasar kan yada labarai da hulda da jama’ a Laolu Akande ne ya fitar da rahoton hakan.

Rahoton yace za’a fara biyan masu koyon sana’ar hannun da aka tantancedon taimaka musu karkashin shirin MSMEs Survival Fund.

Haka nan rahoton yace za’a fara biyan kashin farkon ranar Talata daga mutanen da suka fito daga Abuja, Lagos, Ondo, Kaduna, Borno, Kano, Bauchi, Anambra, Abia, Rivers, Plateau, da jihar Delta.

Kashin farkon sune suka mika takardunsu daga ranar 1 ga watan October zuwa 10 ga watan na October.

Shirin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin kula da shirin don karfafa tattalin arzikin kasar a watan Maris na shekarar nan.
Haka nan shugaban kasar ya nada mataimakinsa Yemi Osinbajo ya jagoranci kwamitin da kuma ganin an kaddamar da shirin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply