Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Aikin Gina Gidaje 10,000 A Jihar Borno

sadiya umar faruk
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Babagana Bukar Wakil Maiduguri.

A kokarinta na sake gina yankunan da ta’adancin ya shafa gwamnatin tarayya ta kaddamar da aikin gina gidaje 10,000 don sake ginin yankunan da Boko Haram suka lallata a jihar Borno.

Yayin da take jawabi yayin take jawabi wajen bikin bude ayyukan a kauyen Ngom dake karamar hukumar Mafa ta jihar Borno ministar walwala da jin dadin jama’a Hajiya Sadiya Faruk tace wan nan shirin ya nuna yadda shugaban kasa Buhari ke kokarin ganin an samu zaman lafiya a yankin.

Ministar tace tace gwamnatin shugaba Buhari zata gina gidajen 10,000 a kananan hukumomi 10 dake jihar ta Borno.

A nashi jaabin gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Zulum yace a wan nan karon sun samu ayyuka masu mahimmanci a tarihin jihar Borno.
Haka nan yace gwamnatin jihar tayi alkawarin kulle sansanonin yang dun hijira kafin 31 ga watan Mayu na shekarar 2021 kuma wadan nan gidajen zau taimaka sosai wajen maida mutane garuruwansu.

Haka nan yace sunaso hukumar ta kafa ababen more rayuwa a yankunan musamman ruwa, tituna, makarantu da kuma gyara titunan Bama zuwa Mubi, Gombe zuwa Bauchi da kuma titin Goniri.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply