Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Aikin Ruwa A Garin Monguno

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A kokarin da gwamnatin tarayya takeyi na samar da ruwa gay an gudun hijira da rikicin Boko Haram ya shafa gwamnatin ta hanyar ma’aikatar shiyyoyi ta bada aikin samar da ruwa a garin Monguno karshin dan majaalisar yankin Monguno, Marte and Nganzai kan kudi Naira miliyan 560 a karamar hukumar ta Monguno dake jihar Borno.

Aikin rowan na garin Monguno na karkashin ayyukan yankin ta hanyar dan majalisar Hon. Mohammed Taeir Monguno.

Yayin da injiniyan dake kula da aikin Engr Ba’ale Bura yake tarbar gwamnan jihar farfesa Babagana Zulumya bayyana masa cewa aikin rowan zai kunshi madaidaiciyar rijiyar burtsatsai 2 da kuma kanana guda 3mai daukar litar ruwa miliyan 2 wadda zata ajiye ruwa da kuma tankoki ruwa da zaici miliyan 1 wanda zasu samar da ruwa a yankin baki daya.

Haka nan yace idan aka gama aikin ruwan na Monguno aikin zai samarwa yan gudun hijirar dake yankin ruwa tsaftatacce.

Yayin da yake yabawa da kokarin dan majalisar gwamnan jihar farfesa Babagana Umara Zulum yace hakan zai kawo karshen matsalar ruwa a garin Monguno da kewaye.

A nashi jawabin dan majalisar yankin na Monguno, Marte and Nganzai ya godewa takwarorinsa da kakakin majalisar da kuma shugaban majalisar Mr Femi Gbajamila kan taimakon da sukayi masa har aikin ya tabbata a yankinsa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply