Najeriya: Gwamnatin Jihar Yobe Zata Gina Gidaje 1800

yobe 3
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Yobe ta fara aikin gina gidaje 1,800 a kananan hukumomi 17 dake fadin jihar a kokarinta na kyautata rayuwar mutane dake kauyuka da masun matsuguni.

Kwamishinan gidaje na jihar Alhaji Bukar Dauda ne ya bayyana hakan inda yace gwamnatin jihar ta fitar da naira biliyan N7.5 don gina gidajen billion 1, 800 wanda ya kunshi mai dakuna 3, mai dakuna 2 da kuma ginin kauye mai dakuna 2 a kananan hukumomin.

Haka nan yace aikin na cikin kashin farko na gidaje 3,600 da gwamna Buni yace zai gina a fadin jihar a gwamnatinsa.
San nan yace tuni aka fara gina gidajen a Damaturu, Gulani, Bursari, Geidam, Yunusari, Fika, Nangere, Fune, Nguru da kuma Yusufari.

Wasu daga cikin mazauna birnin Damaturu sun tabbatar da fara ayyukan wanda ya nuna cewa gwamnatin da gaske take wajen samar da gidajen ga jama’a.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply