Najeriya: Gwamnatin Jihar Taraba Zata Kafa Cibiyar Horar Da Ayyukan Kiwon Zamani

taraba-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ahmed Umar Gosol, Taraba.

Gwamnatin jihar Taraba ta amince da kafa cibiyar horar da ayyukan kiwon na zamani a jihar. Kwamishinan yada labarai da koyarwa na jihar Danjuma Adamu ne ya bayyana hakan bayan dad a suka gudanar da taro a fadar gwamnatin jihar dake Jalingo wanda mataimakin Eng. Haruna Manu ya jagoranta.

Yace cibiyar zata taimakawa dabbobi da manoman wajen rage rikicin su da kuma karfafaf samarda ayyuka da kuma bin dokar kiwon. Danjuma Adamu ya kara da cewa gwamnan jihar ya amince da samarda takin zamia da huma iri.

Yayin da yake Karin haske kan lamarin kwamishinan noma da ma’adanai na jihar na jihar David Ishaya Kassa yace cibiyar kiwon dabbobin na zamani zata koyawa manoma da makiyayay yadda ake amfani da injinan zamani. Ya kuma jaddadda cewa za’a horar da matasa yadda zasu shuga ciyawa da zasu dinga ciyar da dabbobin.

David Kassa ya yabawa gwamnan jihar Darius Ishaku a kokarin da yake ta fannin noma da samar da iri kamar nasi ridi, shinkafa da kuma takin zamani wanda za’a rabawa manoma a farashi mai rahusa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply