Najeriya: Gwamnatin Jihar Borno Zata Maida Wasu Kauyuka 4 Na Zamani

ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno na shirin sake gina wasu kauyuka 4 da samar da ababen more rayuwa na zamani a kokarinda gwamnatinsa take wajen bunkasa rayuwar jama’a.

Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana hakan yayin da yake hira da manema labarai a garin Auno yayin da yaje ziyarar duba ayyukan da akeyi a kauyen na ginin rukunin gidaje 500.

Wanda ma’aikatar sake gine-gine da maida yan gudun hijira ce take aikin gine-ginen.

Acewarsa ana gine-gine 4000 a duk fadin jihar don maida yan gudun hijira garuruwansu don su cigaba da rayuwarsu a yankunansu.

Haka ya umarci kwamitin gina rukunin gidajen 500 da mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Usman Kadaffur yake jagoranta da aka kafa wata 6 da suka gabata na kokarin an gama aikin cikin lokaci don gwamnatin ta samu ta kaddamar da rabawa ma’aikatan gwamnatin musamman masu aiki a kamfanonin takin zamani, robobi, kayan miya, Soda duk dake garin NJimtilo dake wajen birnin Maiduguri.

A baya gwamnan ya yaje zagayen duba ayyukan da ake gudanarwa a garin Ngamdu da Benishiekh.

Yayin ganawarshi da mazauna garin na Ngamdu inda ake aikin gidajen gwamnan ya roki da a gyara wutar lantarkin da yan kungiyar Boko Haram suka lalata shekaru 6 da suka.wuce, da makarantu, da asibitoci, kasuwanni da tashoshin mota.

A garin Benishiekh gwamnan ya duba aikin hanya da ake gudanarwa inda ya bukaci da a gina magudanan ruwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply