Najeriya: Gwamnatin Jihar Borno Ta Mika Sunayen Wasu Limamai 3 Da Suka Ki Bin Dokar Hana Fita

kadafur
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno ta mika sunayen wasu Limamai guda uku da suka ki bin dokar hana fita a jihar. Mataimakin gwamnan jihar Umar Usman Kadafur ne ya bayyana hakan a hirar da yayi da manema labarai a Maiduguri yayin duba da yadda ake bin dokar a fadin jihar.

Limaman suke Goni Isa na Flatari North, Goni Bashir na Lawan Bukar da Goni Gapchia dake jami’ar Maiduguri.
Yace sun san da dokar hana fitar amma suka fita sallar Juma’a wadda aka hana sakamakon yaduwar cutar COVID-19.

Ya kara da cewa abin damuwa ne ace har yanzu wasu na daukar cutar COVID-19 da wasa shiyasa suke karya dokar.
Haka nan yace zasu aika sunansu zuwa gurin Shehun Borno Alhaji Umar-Ibn Garbai wanda shine shugaban shugabannin gargajiya na jihar don a dakatar dasu daga kara yin sallar jam’i.

Haka nan kwamitin da aka kafa na yaki da cutar zai kama duk matafiyin da yayi aniyar shigowa gari ta barauniyar hanya zuwa cikin jihar.

San nan an rawaito cewa shugaban Limamai na jihar Borno Laisu Ibrahim yayi kira ga malamai dasu kiyaye sallar jam’I a fadin jihar don yaki da cutar COVID-19 a jihar.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply