Najeriya: Gwamnatin Jihar Borno Ta Maida ‘Yan Gudun Hijira 2,800 Garin Mafa

idp
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin jihar Borno tace ta maida mutane 2,800 matsugunan su a garin Ajiri dake karamar hukumar Mafa.

Mutanen sun bar yankin da iyalansu inda suka nemi mafaka a Maiduguri bayan da ‘yan kungiyar Boko Haramsuka mamaye yankinsu fiye da shekaru 5.

Mustapha Gubio kwamishinan maida yan gudun hijira da sake gine-gine ne ya bayyana hakan yayin da yake bada rukunan gidaje 500 ga iyalan da suka koma garin na Mafa.

Gubio yace yan gudun hijirar sun samu mafaka a sansanin dake Customs a birnin Maiduguri wanda har alla yasa suka koma gidajensu don cigaba da rayuwarsu.

Haka nan yace tsarin na maida yan gudun hijirar an gudanar dashi kamar yadda yake a tsarin bada agaji don karfafa tsaron yankin.

Kwamishinan yace kauyukan sun fuskanci ayyukan ta’addanci da aka lalata musu gidajensu inda a yanzu gwamnatin ta samu ta gina musu hade da samar da abubuwan da suke bukata.

Gubio yace ma’aikatarsa ta samar musu da abinci da kayan agaji kamar shinkafa, mai gidan sauro abun rufa kayan sawa da katifu.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply