Najeriya: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Sassauta Biyan Haraji

map-of-bauchi-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Fatima Idris Danjuma, Bauchi.

A cigaba da saukakawa mutane sakamakon annobar COVID 19 gwamnatin jihar Bauchi ta dagewa mutane biyan haraji a jihar.

Shugaban hukumar harajin jiha Alh Muazu Usman ne ya bayyana hakan ga manema labarai ranar lahadi a jihar inda yace gwamnan jihar Bala Mohammed ne ya amince da hakan.

Haka nan yace an dage biyan harajin ga wadanda aka kara musu lokacin biyan harajin yayinda za’a hada rahoto shekara ga masu biyan.

San nan an sassautawa wadanda suke da laifinrashin biyan harajin na guraren da sai sun samu kudi suke biyan harajin otel- otel, guraren cin abinci, tashoshin mota, makarantun kudi da wadanda duk basu biya harajin daga watan Januiru zuwa watan Yuli na wan nan shekarar.

Alh Muazu ya kara da cewa an sahalewa wadanda basu biya kudaden da wuri ban a wata 12 wanda ya fara daga daya ga watan January na shekarar 2020,inda aka amince daga watan na Janairu na shekarar 2020 zuwa watan Disamba 2020.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply