Najeriya: Gwamnatin Jihar Adamawa Zata Horar Da Matasa 500 Sana’oi

adamawa-state
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Hassan Umar Shallpella

Gwamnatin jihar Adamawa ta kammala shirye-shiryen amfani da cibiyar horarwa ta moribund Technical Centres dake jihar don harar da matasa 500 a sana’oi daban daban a fadin jihar.

Matasan zasu koyi sarrafa abubuwan amfani a cikin jihar ta Adamawa.

Matasan 500 za’a koya musu sana’ar aski, kiwon kifi, kiwon kaji, sarrafa abinci da ajiye shi, hada sabulai, kwalliya, daukar hoto, da sauransu.

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ne ya bayyana hakan a babbar makaranta General Murtal Muhammad College dake Yola.

Yayin da yake jawabi kan horar da matasan 500 gwamnan yace kashin farko zasu samu horon karkashin hukumar rage radadin talauci.

Haka nan gwamnati ta ware fili kimanin hecta 100 a kowace karamar hukuma don samar da cibiyoyin da matasan zasu baje kolin bajintarsu don amfanin jihar.

Haka nan Gwamna Fintiri ya bayyana cewa gwamnati ta samar da ilimi kyauta, da bada abinci kyauta da biyan tallafi ga daliban manyan makarantu da kuma gyara da sake gine-ginen qasu azuzuwan don komawa makarantun.

A nata bangaren shugabar hukumar rage radadin talauci Hajiya Aishatu Bawa Bello tace wadanda zasu amfana su 2000 ne amma sun rage sakamakon annobar COVID-19 wanda yasa dole suka raba kashi- kashi.

Shugaban British Council na ofishinsu dake Yola Abdulkadir Bello Ahmed ya yabawa gwamnatin jihar kan samarwa matasa abunyi.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply