Najeriya: Gwamnan Jihar Taraba Darius Dickson Ishaku Ya Yabawa Hukumar Zaben Jihar

darius-ishaku-690x450-1
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Ahmed Umar Gosol, Taraba.

Gwamnan jihar Taraba Darius Dickson Ishakuyace zai cigaba da bawa kananan hukumomi mahimmanci saboda yadda suka fi kusa da talakawa.

Gwamnan ya bayyana hakan yayin da yake jawabi yayin rantsar da sababbin shugabannin kananan hukumomin da akayi a kananan hukumomi sha shida a jihar wanda aka gudanar a makarantar firamare ta Rimi dake Takum.

Yayin da yake taya sabbabin shugabannin murna gwamna Darius Ishaku yace yadda aka fito zaben ya nuna yadda shugabannin suke da jama’a kuma yai kira garesu dasu gudanar da gaskiya kan yadda aka yarje musu.

Haka nan ya yabawa mutanen Taraba kan yadda suka gudanar da zabe cikin zaman lafiya da lumana kafin zaben da kuma bayan zaben.

San nan Governor Ishaku ya yabawa hukumar zaben jihar yadda ta gudanar da zaben duk da matsalar tattalin arziki da ake fama dashi a duniya baki daya sakamakon annobar COVID -19.

A nashi jawabin shugaban shugabannin kananan hukumomin na Najeriya Abdulnaseer Bobboji ya godewa Gwamna Darius Ishaku, jam’iyyar PDP da kuma mutanen jihar Taraba kan yadda suka dauki zaben kuma ya tabbatar musu cewa zasu samar da abubuwan bunkasa rayuwar su tun daga kasa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply