Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Tabbatar Da Mutuwar Mutane 81 Bayan Harin Boko Haram

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamna Babagana Zulum na jihaar Borno ya tabbatar da mutuwar mutane 81 bayan harin day an kungiyar Boko Haram suka kai kauyen terrorists Faduma Koloram dake karamar hukumar Gubio ranar Talata.

Gwamna Zulum ya bayyana hakan bayan daya kai ziyarar jaje inda abun ya faru don jajantawa wadanda suka tsira daga harin.

Gwamnan ya bayyana cewa mutane 13 ne suka samu raunuka yayin da suke tserewa daga harin inda 7 daga cikinsu ne suka samu raunuka da dama.

Ya kara da cewa kafin ya isa tuni aka binne mutane 49 inda yanuwan ragowar 32 yanuwansu suka dauki gawarsu.
Gwamnan ya bayyana harin a matsayin abun takaici inda yace hanyar da za’a kawo karshen wannan kisan itace idan aka kakkabe yan ta’addan daga yankin tafkin Chadi gaba daya.

Zulum ya kara da cewa gwamnatin jihar zata dauki nata matakan na kare mutane daga faruwar irin wan nan hare-haren ta hanyar hada manyan garuruwa da kanana ta inda za’a samar da tsaro.

DANDAL KURA RADIO INTERNATIONAL ta rawaito cewa an yi zana’izar bai daya ga wadanda suka rasa rayukansu a harin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply