Najeriya: Gwamnan jihar Borno Ya Kafa Kwamitin Rabon Kayan Tallafi

photo by Babagana Bukar Wakil Ngala

photo by Babagana Bukar Wakil Ngala

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya kafa kwamiti mai mutane goma sha shida wanda zai raba kayan abinci don rage radadain zaman gida da aka kafa na kwana goma sha hudu a jihar.

Mai bawa gwamnan shawara kan hulda da jama’a Malam Isa Gusau ne ya bayyana hakan a sakon daya fitar ranar Juma’a.
Gusau yace kwamishinan noma Engr Bukar Talba ne zai jagoranci kwamitin inda za’a rabawa mutanen dake da bukatar taimakon sakamakon zaman gida da akeyi don dakile cutar Covid-19.

Ya kara da cewa shugabar hukumar bada agaji ta jiha Hajja Yabawa Kolo ce sakatariyar kwamitin, sai kuma mammbobin kwamitin su sha hudu.

Hakanan ya bayyana cewa Gwamna Zulum ya bukaci yan kwamiti dasu gudanar da aikin da aka dora su akai tukuru da kuma tsoron Allah.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply