Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Kafa Kungiyar Sa Ido Ta Neighborhood Watch

borno state small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sakamakon sace sace da lalata kayan gwamnati da akeyi a jihar Borno dake Najeriya gwamnan jihar Kashim Shettimaya kaddamar da yan sa ido masu suna Neighborhood Watch.

An samo yan Neighbourhood Watch daga yan kungiyar sa kai na CJTF da suka fara aiki tun shekarar 2013 sakamakon yaki da yan kungiyar Boko Haram.

Yayin bikin an samu matasa 2,900 daga unguwoyi 25 dake cikin birnin Maiduguri da Jere, Gwamnan yace an samarda kayyakin more rayuwa da yawa kamar wutar kan titi, kayan aiki da rana da kuma baturansu don haskaka tituna da karfafa tsaro amma wasu na sacewa ko su lalata.

Haka nan ya kirayesu dasu guji daukar doka a hannunsu, sannan ya basu motar sunturi 25 inda yace su dinga bada taimakon gaggawa na kai mutane asibiti cikin dare da kuma masu haihuwa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply