Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Kaddamar da Rabon Takin Mamani Ga Manoma

ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwaman Babagana Zulum na jihar Borno ya kaddamar da rabon takin zamani na tan 300 ga manoma don fara ayyukan noma a fadin jihar.

An fara rabon da wuri wanda yazo dai-dai lokacin da manoman suke fara shuka a watanYuli. Yayin kaddamarwar da akayi a satin mako a Kwaya Kusar mataimakin gwamnan Umar Kadafur wanda ya wakilici gwamna Zulum yace domin tabbatar da an samunasara a rabon an kafa kwamitin da zai duba rabon takin a kananan hukumomi 27 dake fadin jihar.

Kwamishinan noma na jihar Alhaji Bukar Talba ya bayyana cewa motoci 180 dauke da takin za’a rabawa shiyyoyi tara dake kudancin jihar.

Haka nan yace ko wane yanki zai samu mota goma ga manoman yankin. San nan tsakiyar da Arewacin yankin zai samu 40 da 50 na motocin inda wasu zasu samu 8 wasu 10.

Ya kara da cewa wan nan na daya daga cikin ayyukan gwamnatin gwamna Zulum guda 10 san nan rabon takin zai habbaka rayuwan manoman dake kauyuka.

Kadafur yayi alkawarin samar musu da kayan noma kamar motocin noma, tankin ruwa, maganin feshi da zai kare shukokshin.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply