Najeriya: Gwamnan Jihar Borno Ya Amince Da Biyan Naira Miliyan 624 Don Biyan Kudaden Scholarship

photo by Babagana Bukar Wakil Ngala

photo by Babagana Bukar Wakil Ngala

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Kwamishinan mayan makarantu na jihar Borno Professor Isa Hussaini Marte inda yace Gwamnan jihar Babagama Umara Zulum ya amince da Naira miliyan 624 don biyan kudaden scholarship na dalibai 23, 776 daga makarantu 48.

Haka nan yace za’a bawa daliban masters su 166, masu degree 11,790 masu diploma 883, masu NCE 3,015, MASU ND 6,897 sai kuma 1037 masu HND.

Kwamishinan ya bayana hakan yayin taromn da aka gudanar na bikin shekarar gwamnan daya kan mulki a dakin taro na multipurpose hall dake fadar gwamnantin jihar dake Maiduguri ranar Laraba.

Haka nan yace masu degree na farko za’abasu N50,000 zuwa N100,000 daga jami’ar jihar, makarantun gaba da sakandire, makarantar makafi.
San nan ya tabbatar da kafa jari na musamman a harkar ilimi a jihar kafin karshen gwamnatin Gwamna Babagana Zulum inda suke sa ran zata fi kowace kasa a fadin Najeriya.

Kwamishinan ya bayyana cewa yana da tabbacin cewa jihar Borno zata kai matakin day a dace ta fannin ilimi indai farfesa Zulum ne gwamnan jihar .

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply