
By FATIMA IDRIS, BAUCHI
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi yayi kira ga jami’an tsaro dake aiki a jihar su karfaffa sha’anin tsaro a yankuna masu hatsari.
Gwamnan yayi kiran bayanda kwamandan rundunar sojin sama na jihar Air Vice Marshal Charles Ohwo yakai masa ziyara a fadar gwamnatin jihar dake Bauchi kan gyaran jiragensu a filin saukar jirage na Tafawa Balewa.

Gwamnan ya jajanta da kisan dayan bindiga suka yiwa dan majalisar tarayya a jihar Honourable Musa Mante Baraza inda yace gwamnatinsa a shirye take ta taimakawa jami’an tsaro wajen yaki da ta’addanci a jihar.
Haka nan yace gwamnatin jihar zata taimakawa jami’an tsaro da kayan aiki don samun saukin kasha mutane.
A nashi bangaren kwmandan rundunar sojin saman Air Vice Marshal Charles Ohwo yace sun kai ziyarar ne kan wasu sababbin tsare –tsare da zasu amfani jihar.
