Najeriya: Gwamna Zulum Yayi Kira Ga Musulami Da Susa Boko haram Cikin Addu’oinsu

ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum yayi kira ga musulman jihar Borno dana kasa baki daya dasu sa Boko Haram da masu daukar nauyinsu da kuma masu mara musu baya cikin ayyukan ta’addanci yayin sallolinsu na ‘Tahajjud’ bawai cutar Coronavirus kadai ba.

Rahoton ya fita ta hannun mai Magana da yawun gwamnan Malam Isa Gusau a Maiduguri a jiya. Inda yace yawancin Musulmi hankalinsu na kan annobar Coronavirus, ya kamata su sa Boko haram a ciki albarkacin wan nan watan na Ramadan musamman a goman nan na karshe.

Yace ba tantama annobar COVID-19 mai tada hankali a rayuwar dan Adam don haka dole a gudanar da addu’oi a kanta don haka ne yayi wan nan kiran musammmanwadanda suke jihar Borno da kuma ragowar jihohin Arewa maso gabas. Ya kara dace idan aka mika kai ga Allah Allah zai taimaka don babu cutar da bata da magani.

Gwamnan yace addu’a kan Boko Haram abu ne day a zama dole a halin yanzu kbayan da jami’an soji day an kungiyar sa kai na civilian JTF da maharba day an sa kai suke samun nasara a yakin da suke da ta’addan.

Haka nan gwamna Zulum yayi kira ga mutane masu hannu da shuni dasu taimakawa masu karamin karfi musamman yan gudun hijira, marayu, wadanda mazajensu suka rasu, yanuwa da makota musamman a watan nan na Ramadan.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply