
By:Babagana Bukar Wakil Ngala, Maiduguri
Gwamna Babagama Umara Zulum na jihar Borno ya samar da manyan gonakin noma a kananan hukumomi goma dake fadin jihar masu girman hekta 3,611 cikin watanni 12.
Kananan hukumomin sune Konduga, Ngala, Dikwa, Biu, Askira/Uba, Magumeri da Kaga. Inda aka noma shinkafa, masara, gyada, gero, ridi da sauransu.

Kwamishinan noma da ma’adanai na jihar Engineer Bukar Talba ne ya bayyana hakan yayin taron da aka gudanar na shekarar gwamnatin jihar daya a fadar gwamnatin dake Maiduguri .
Yace an samar da tsarin ne don karfafawa manoma gwiwar komawa yankunansu da gonakinsu da kuma bawa jami’an tsaro bayani ta hanyar Agro Rangers, yan kungiyar sa kai, maharba da kuma yan CJTF.
Haka nan yace ma’aikatar ta gyara motocin noma 58 da kuma gina wasu yankunan ayyukan karafa guda 4.
San nan Engr. Talba yace a kokarin ma’aikatar na kare injinan ta gina musu rumfuna da kuma samar da injinan ruwa domin noman rani a garin Damasak da garin Biu.
