Najeriya: Gwamna Zulum Ya Rantsar Da Shugaban Ma’aikata Farfesa Isa Marte

FB_IMG_1597837434341
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwaman jihar Borno farfesa Babagana Zulum ya rantsar da farfesa Isa Marte a matsayin sabon shugaban ma’aikata da Abba Sadiq a matsayin dan hukumar Shari’a ta jihar.

Gwamna Zulum yace ya basu mukaman ne bayan shawarwari da ya samu da kuma duba da yayi cikin tsanaki.

Haka nan yace yayi duba da cancantarsu, kokarinsu da kuma amanna da ake dashiakan ayyukansu.

Gwamnan ya bukaci wadanda aka bawa kukaman dasuyi amfani da kwarewarsu wajen cigaban gwamnatinsa

san nan ya jajanta da rasuwar tsohon shuga an ma’aikatan Babagana Wakil da kuma yabawa ayyukan da ya gudanar a lokacinsa.

A nashi bangaren Marte ya godewa gwamnan kan yadda da yayi dasu har ya basu aikin.

Kuma ya bayyana gwamna Zulum a matsayin shugaban da kullum yake samarwa mutanensa mafita da cigaban jihar da kuma habbaka rayuwar mutanensa.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply