Najeriya: Gwamna Zulum Ya Kai Kayan Tallafi Kala Balge

ZULUM
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnan jihar Borno farfesa Babagana Zulum ya jagoranci rabon kayan abinci ga 10,000 a garin Rann dake karamar hukumar Kala-Balge.

Gwamnan yayi tafiyar daga Maiduguri zuwa Rann a jirgin sojoji mai saukar ungulu zuwa karamar hukumar wadda take da iyaka da kasar Kamaru.

Wan nan ne karo na hudu da gwamnan ya kai ziyara yankin inda ya farauwa a watan Yuni na shekarar 2019 kwanaki kadan bayan an rantsar dashi, yayin da yaje duba ayyukan day a kamata a yi a yankin.

Haka nan ya koma a watan Disamba na shekarar 2019 don rabon kuddade naira 15,000 ga matan da suka rasa mazajensu sai kuma komawar da yayai a watan Fabarairu na wan nan shekarar don rabon naira miliyan 100 inda kowa ya samu 10,000.

A wan nan ziyarar ta wan nan karon gwamna Zulum ya duba yadda ake rabon kayan abincin musamman ga mata da tsofaffi da kuma masu bukata ta musamman inda kimanin yan Najeriya 300 dake zaman hijira a kasar kamaru suka zo Rann karbar tallafin.

Kowannne mutum daga cikin wadanda suka amfana ya samu Each buhun masara, kwalin taliya 2, karamin buhun shinkafa 2, man girki mai lita 3, inda aka karawa mata da atamfofi akan kayan abincin.

Mazauna garin Rannsun makkale a garin sakamakon rashinhanyar mota sakamakon ambaliyar da aka samu daga kogi wanda ya hana noma har wasu suka koma kasar

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply