Najeriya: Gwamna Zulum Ya Kaddamar Da Aikin Ruwa Na Naira Miliyan 200 A Unguwar Gwaidangari

zulum
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya kaddamar da aikin Naira miliyan 200 a unguwar Gwaidangari da Shehuri North Community duk.a.cikin birnin Maiduguri wanda gidauniyar Jack Rich ta samar.

Haka nan yayi alkawarin ginin sabon titi daga titin Baga zuwa unguwar ta Gwaidangari da sabuwar rijiyar burtsatsai da alkawarin cigaba da samar da abubuwan more rayuwa a yankunan jihar

Gwamna Zulum ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin ruwan da mai bada ataimakon ya dauki nayiwanda yake dan kasar Amurka karkashin gidauniyarsa da take taimakawa marasa karfi cikin al’umma.

Haka nan yayi kira ga shugabannin al’ummar Gwaidangari dasu kula da ayyukan da mahimanci.

san nan ya umarci ma’aikatar ruwa da ma’adanai ta jihar da ta bada sunayen hanyoyin ruwa na jihar a dukkanin kananan hukumomin 27 wanda na cikin kudirin da gwamnatin take so ta cimma.

Gwamnan ya godewa mai bada taimakon injiniya
Jack Rich da wan nan tallafin ga mutanen jiharda kuma taimakon da yake bayarwa ta fannin ilimi, lafiya, hanyoyi, samar da ruwa a kasa baki daya.

Haka nan ya godewa tsohon sakataren kasar Ambassador Babagana Kingibe kan kokarinda yayi na gudanar da ayyukan da kuma Injiniya Jack Rich da bada taimakon.

Download Our App from the Google Play Store

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Latest news

Leave a Reply